Tuesday, January 29, 2019

Wata amarya CE



Wata amarya da mijinta sukaje bankin zenith domin su cire wani kudi. Ko da amarya tazo shiga se kawai muka ji wani alam me karfin gaske, jin haka se ga ‘yan sandan bankin su fito da gudu da bindigun su! Ai ina ganin haka se na tsure! Sun kamani ni da matata wai basu yarda damu ba shisa zasu kai ofishin ‘yan sanda sun bincike mu! Munje har anyi sacin dina amma basu ga komai ba! An zo kan matan ana sacin dinta kawai se ga gwangwanin milo babban ya fado daga kanta! Dani da ‘yan sandan ba wanda ze kama wani gurin gudu, domin kuwa mun dauka bom ne ya fado ashe wai acuci mazanta ne ya fado! Wannan jaraba dame yayi kama??? Shiko D.P.O be ma dawo cikin hayacin sa ba tsabar tsorata da yayi.

Jiya ina kwance da misalin karfe 2:30/am   na dare ina bacci sai na farka. Ina farkawa sai naji hayaniyar mutane a waje sai na fito amma banga kowa bahSai na koma daki na kwanta amma ban daina jin hayaniyar ba sai mah karuwa takeyi Na sake fitowa a karo na biyu but banga kowa bah.....Kamar ance in kalli sama,ina duba sama kuwa sai naga mutane Wai ashe jirgin sama ne ya lalace shine suke turawa Saura kuma kuce karya Nake.

Wata tsohuwa ce suka je kasuwa da karamin jikanta, sai jikan ya dauki motar wasa sai tsohuwa tace digiri ajiye motar nan, sai mai kaya ya tambayi tsohuwa: sunanshi digiri? Tsohuwa tace: mamanshi na tura   jami'a ta dawo min dashi

No comments:

Post a Comment