Tuesday, January 29, 2019

Wani bawan Allah me mai tsananin kamun kai


Wani bawan Allah ne mai tsananin kamun kai, wanda yake zaune a wani gidan haya da matarsa, sai watarana matarsa ta tafi unguwa shi kuma sai ya shiga bayi yayi wanka sai ya rataye tufafinsa akan katangar bayin don bayin budadde ne babu rufi. Sai wani 6arawo yaga tufafin sun leqo waje sai ya janyesu ya tsere ta lungu.
Mutumin bai tashi sanin an sace tufafinsa ba har sai da ya gama wankansa zai fito sannan ya ankara don haka sai ya tsaya shiru ya rasa abin yi don yaji motsin matar abokin zamansa tana kwashe shanyar tufafinta dafa shanya a igiyar shanyar dake tsakar gida kusa da bayin saboda tasowar iska kar ya zubar mata da tufafin. Ana cikin haka sai kuwa iskar ta dauki wani fallen zaninta ta jefa matashi bayi inda mutumin nan yake ciki.
Ai sai mutumin yayi murna ya dauki zanin matar wani ya daura don ya rufe tsiraicinsa dashi sai ya fito da sauri daure da zanin matar wani a qugunsa kuma gashi baya yin magana da matar auren gidan, sai ya nufi dakinsa da sauri ita kuwa mai zanin sai abun ya daure mata kai tana ta kallon zanin sallan da mijinta ya dinka mata a qugun wani mutum wanda ba mijinta ba.
Mutumin na isa dakinsa sai ya tuna ya ashe ya rufe dakin da makulli kuma makullin na cikin aljihun wandonsa da aka sace sai ya tsaya a jikin qofar yana salati don duk kayansa suna cikin dakin. Chan sai matarsa ta dawo unguwa taga mijinta da zanin matar hayar gidan sai ta tayar da rigima akan alanbalan yana neman matan gidan don su biyu aka bari a gidan kuma ga zani shaida a qugunsa don haka tabbas kwartanci yaje sukayi a dakinta har ya daura zaninta.
Ana cikin hayaniya sai mijin waccan matar da aka daura zaninta ya shigo yaga abin dake faruwa shima sai ya tayar da rigima har kotu da qyar Allah Ya fid da mutumin nan bisa shaidar tufafinsa da aka kaiwa wani dillali sayarwa shi kuma ya gane mai su don yasan ana rigimar shine ya kawosu kotu tare da yin cikakken bayanin da tasa aka kama 6arawon sannan aka wanke mutumin daga zargi.
*Ya Allah Ka qara tsaremu daga afkawa cikin kowane irin musibah, ameen.

No comments:

Post a Comment