Tuesday, January 29, 2019
A BIYO MU A LITTAFI NA GABA.
Wani mai share cikin jirgin sama ne mai karambani bayan ya shiga jirgi don yin goge-goge kamar yadda ya saba, sai ya tarar da wani littafi mai taken: “YADDA AKE KOYON TUkIN JIRGIN SAMA A SAUkAkE.”
Yana bude shafin farko sai ya ga an rubutu “Idan aka danna, kaza da kaza, za a tayar da injin jirgi. Sai ya danna, injin jirgi ya fara aiki. Sai ya bude shafi na gaba, nan kuma aka rubuta “Idan aka danna kaza da kaza, jirgi zai fara tafiya, nan ma ya danna, jirgi ya fara tafiya.
Can da ya bude shafi na gaba, sai ya ga an rubutu “Idan aka danna kaza da kaza jirgi zai yi sama, nan ma ya danna jirgi ya tashi sama da shi. Da ya bude shafi na gaba, sai idonsa ya raina fata don ya ga an rubuta “Don jin yadda jirgi ke sauka sai a biyo mu a littafi na gaba!”
SAURAYI DA BUDURWA 1.
Wani saurayi ne da budurwarsa suka yi hira kamar haka:
Saurayi: Ladidi an tashi lafiya?
Budurwa: Ta yi biris kamar ba ta ji shi ba.
Saurayi: Ladidi an kusa daura mana aure amma har yanzu ba ki daina yi min wulakanci ba.
Budurwa: Ta sake biris.
Saurayi: Dama ba wani abu ne ya kawo ni ba illa in tambaye ki ko kin iya tuki. Domin ina son matata ta kware a tuki
Budurwa: Nan da nan ta amsa cewa Tanimu ke nan shi ya sa nake matukar sonka.
Saurayi: Uhmm…
Budurwa: To wace irin mota za ka saya min?
Saurayi: Mota kuma?
Budurwa: Eh mana, ba yanzu ka tambaye ni ko na iya tuki ba?
Saurayi: Ni fa tukin tuwo nake nufi don wani masoyina ne ya ba ni kyautar buhun masara.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment