Thursday, January 31, 2019
soyayya Ce zallah
Sarauniyata taho gare ni ki kama hannuna ki furtamin kalmar kauna a cikin kunnuwana…na rayu saboda ke ki zo ki mutu a kai na…ki sani ni fa ko a lahira idan an tashe mu to ke nake so a matsayin matata….na samu biyayyarki me kuma ya rage zan roka a wajen ubangiji?
kawai numfashi nake so ga ubangiji don mu yi soyayya mai dorewa ni da ke….fatana Allah.ya tsawaita mana rayuwa ya ke abar kaunata…wacce nake ganin sunan ‘ya’yan da zan haifa a cikin idanuwanki….fakina da idanuwana ba za su iya fada miki ko kwatanta miki adadin son da nake miki ba don tuni na shide a cikin sonki, na zama ke….
Ke dai taho gare ni dauke da kauna za ki gane ni ne na ki..ba ni da ta cewa sai godia ga Allah da ya ba ni yar fara mai fararen idanuwan da suka dace da kyakkyawan hancinta wanda ya yi daidai da kyakkywan kumatunki…wanda ya sa kika zarce sauran mata a kyau.
Ya ke mai kyakkyawar kirar jikin da babu irinki..mai iya kwalliya tamkar dawisu..mai zakin murya kamar kanari..takawarki lafiya mai tafiyar aasaita tamkar jimina kin isa ne dole ki yi domin duniya ban ga kamar ki ba ko kusa babu ba aiba kuma ba za ai ba
Ya ke rayuwata na dauki amanarki daga nan har izuwa ranar tashin alkiyama, ya ke wadda saboda tsananin kyauta idan tana tafiya ba takalmi samaniya ke ji kamar ta sakko kasa ki takata don ta ji me doran kasa ke ji.
Ke dai bari kawai ki sha kuriminki ni na ki ne ke tawa c,e kuma mun riga mun yi alkawari…ni da ke ke da ni jiki biyu ne muka zama rai daya zuciya daya…ba rabuwa har abada wannan shi ne alkawarina fatana ga mahalichchinmu ya cika mana burinmu. Sarauniya rife bakinki ba sai kin ce komai ba zuciyarki da gangar jikinki da kyawawan fararen idanuwanki su riga sun sanar da ni irin tsananin son da kike min don haka kwantar da hankalinki ba sai kin fada ba na san ba zai kwatantu ba ke dai samu guri mai kyau a cikin zuciyarki ki kara boye ni kawai domin ni na ki ne ke kadai
Hanya daya da zan bi na kwantar miki da hankali ita ce abin da kin riga kin sani kuma zan kara jaddada miki shi ne…..idan ba ke ba ni idan ba soyayyarki ba nimfashina duk wata ya budurwa a idanuwana fanko ne domin ke kadai nake gani na san na ga ‘ya mace kin ga idan ba ke a tare da ni ba zan iya gane ni da namiji ba ne don haka ni na ki ne mai sonki har abada soyayyarki ce jagorar rayuwata matukar ba soyayyarki to ba zan amfana ba kidai rike ni amana, ni ne dai na ki wanda ya zama ke, kika zama shi.
M asoyiyata abar kaunata ki sani ina sonki ina kaunarki son da nake miki har ya kai ga…..ko da idanuwana a rife suke ke nake gani idan na bude su ke nake son gani. Ko da ba na tare da ke ina jin motsinki a cikin jikina Lokachin da nake tinaninki, kadaici shi ya fiye min komai dadi. Me ya sa kina rayuwa a cikin jikina ni ma ina rayuwa a cikin jikinki amma duk da haka nake jin tsakaninmu da nisa?
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment