Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda uku 1,2 da 3.
Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan kaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika boye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya kin ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena. Duk wani taku da na yi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min suka.
Ganinki burina, idanuwana ko bacci na farka ki amshi soyayyata abadan kada na koka ba ni barinki cikin kunci yaki zo na yi miki tarba. Daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa a duk zantukana sai na ambace ki. Damuwarki kullum tana cikin tinanina ke ce jin dadina kuma ke ce bacin raina ke kadai ce a zuciyata kalamaina, zabina jin dadina, bacin raina, saboda da ke kawai nake rayuwata, kaunarki ce ke kula da ni take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni ka san tuwata zan zamana a tare da ke har abada. Kamar yanda baki bai isa ya furta ba haka jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciya ta yi kadan ta kwatanta ruhinki ne kadai ya san yadda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowane dare ina sonki ba zan daina ba har abada saboda ban isa na daina ba.
Soyayyata da ke ba ta mutuwa kuma ba ta tsoran mutuwa koda za a yi mana kwace, ko da za mu mutu ko za mu lalace to soyayyar mu za ta kasance a raye na bayar da zuciyata na karbi ta ki na kamu da sonki. Ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da ta shagala a kan tsananin soyayyarki ka da rintsi ko zugar mahassada ya sa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke dankare a kan dan’adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake miki.
Labarin Zainab Da Mubarak (7)
Har zuciyarsa ta burge ta sosai don ya iya tsari sai dai kuma ta san ba zai yiyu ta aure shi ba, cikin sauri ta kawar da wannan tunani ta ce “ai na za ta ba zuwa za kai ba, sai dai shi har yanzu ya kasa daina kallonta, shi ma kwalliyar da ta yi ta dauke hankalinsa gaba daya. Wani Material ta saka (Purple) wanda aka ratsa masa (pink colour) a jiki, dinkin riga da siket sai kuma ta dauko (pink) din mayafi ta dora a kai shi ma takalmin ya dace da mayafin jikinta, a hankali ya saki ajjiyar zuciya tare da murmushi ya ce “ Ni na Isa?, kin san ganinki ya fiye min komai” Sai fa ya zuba wa Zeey ido da colour da ke gefen precious wani irin wanda ya sa duk ta bi ta tsargu don kunya, ta sunkuyar da kanta ya ce “’yan mata adon gari, kin yi shiru, ko rowar muryar ake mana?” Ita dai Zeey colour ji take tamkar mafarki take yi, don ta tabbata duk wanda ya ga Seif dole ne ya yaba tsarinsa, precious ta yi gaskiya Saif yana da kyau sosai kuma gashi ya iya kwalliya don duk ya hada komai na kyau wanda ake bukatar a ga da namiji da shi, fari ne kyakkyawa na kin karawa, gashi dogo, hancinsa dogo, bakinsa dai-dai misali, idanuwansa gwanin ban sha’awa, gashin kansa akwance yake irin na Fulani.
Hasali ma ga iya furta zance sai dai kuma abin da ta lura da shi akwai jiji da kai hakan kuwa ba ya daga cikin tsarinta. Ta kale shi ta yi shiru na dan wasu dakiku kanar ba za ta yi magana ba, daga bisani kuma ta ce “Uhm..! Ya kake?, ya kuma hanya?”, Saif ya ce “ Lafiya lau, ina fatan dai kina kula min da baby na ko?” Ita dai Zeey colour har ta kagu tabar wajen ta koma ciki, a ganinta ya fiya kallo, a hankali ta danyi murmushi ta ce “Kamar ka sani, kullum ni nake kula da ita”, Precious kuwa har zuciyarta ji take kamar tafi kowa farin ciki don ganin gata ga Saif , cikin fara’a precious ta ce “ Wannan ita ce kawata Zainab ana kiranta da Zeey colour wadda nake ba ka labari ba ni da Aminiya kamar ta” Saif ya tsura mata idanu yanayin yanda take magana yana burge shi hakan ya sa ya ci gaba da saurarenta tare da bin kallon bakinta da yake motsi…
No comments:
Post a Comment