Tuesday, January 29, 2019

An FASA kwai

*

**AN FASA KWAI***
Wani mutum ne yayi sabuwar amarya sai ya dauketa ya kaita wani hotel don suyi honey moon dinsu a chan, watau suci amarcinsu a tsanake inji sa'ad khalifa yakubu (sky) .
suna shiga hotel din sai mutumin ya ajiye amaryar tasa a falo don yaje reception ya biya kudin daki ya kar6o makulli. Zaman amaryar keda wuya sai wata karuwa tazo wurinta ta sameta tace "sannu 'yar-uwa naga waccan macucin mutumin kema ya kawoki nan ne ku kwana (ta nuna mijin) toh kar ki sake ya kwana dake bai biyaki ba (ta dauka itama karuwa ce) kiyi maza ki amshi kudinki tun da farko don guduwa yakeyi baya biya don ni shaida ce saboda munsha kwana dashi baya biyana. kuma ki tambayi kowace karuwa a hotel dinnan kiji don kusan duk ya nemesu suna kwana dashi yana guduwa baya biya. kema don naga baquwa ce baki san halinshi bane har kika biyoshi zaku kwana ya cuceki. gashi da shegen neman karuwan tsiya kamar bunsuru don ni tuni ai na gujeshi kar yasa mun qanjamau don naji ana rade-radin wai yanzu ya kamu da qanjaman don cikakken 'Dan-duniya ne"
*Wai in kece amaryar ya za kiyi tun baku tare ba? za kiyi kasada ne ku kwana sannan ki tabbatar ko kuwa ya ya???
*KIWON LAFIYA
(yadda zaka cire targade da kanka)
Ka sami igiyar kyalle mai karfi sai ka daure yatsar mai targade a wani turke kamar na rumfa, sai ka fizgi yatsan da karfi fizga daya idan kayi da kyau targaden zai fita. Yadda zaka gane fitarsa shine za kaji yayi qara 'qas' alamar ya fita ya gyaru kenan, sai ka sami mantaleta ka dirza a wurin targaden. Da safe ka gasa da ruwan zafi da tawul kasa mantaleta shikenan. Idan bai fita ba yayi qara ba sai ka sake kwatantawa har a dace shikenan.




BAZAZZAGI DA LARABCI.
Wani Bazazzagi ne suka hada kudi da Balarabe suka sayi jakai guda
biyu suna kiwo. Kuma ya kasance Bazazzagi ke yin kiwon wadannan
jakuna guda 2. Kwatsam wata rana sai aka yi ruwa ya cika gidan Bazazzagin nan, har jakunan suka mutu. Ya je ya samu Balarabe, yana so ya yi masa Bayanin cewa ruwa ya cika masa gida har jakunan sun mutu. Suna haduwa sai ya ce masa: “Wa himaruka wa himariy, al ma’u bulbula fiy baitiy, mautu jami’an.”

No comments:

Post a Comment