Thursday, January 31, 2019

massoyiyA ta



1. TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.

2. KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.

3. KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.

4. KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana ɗaya ba, ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haɗu sau uku. Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare. Wani lokacin idan haɗuwa ta yi ƙaranci sai ka kirata a waya. Amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura. Ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi ƙarfi ba.

5. KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN ƘAWAYE: Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun ƙawayenta ko kuma cikin jama’a. Hakan zai karama kima, sannan da nesan ta kanka ga barin wulakanci. Wata kila lokacin da ka je mata cikin jama’a ko ƙawayen ta, ta ji tana son ka. To amma watakila a lokacin shigar da ka yi bai yi mata ba. Hakan zai sa ta guje ka, wanda yin haka a soyayya wulakanci ne ga masoyi.

Mafi kyawu shi ne ka jira ta keɓance ko kuma ta koma gida. Idan ba haka ba, to sai dai idan sun kai koda su biyar ne, to kuma ya zama dole ku kasance ku biyar koda sauran ba sa san ‘yan matan. Saboda su kasance masu ɗauke masu hankali a lokacin da kuke hira kuma suma sauran ‘yan matan yin haka zai nuna cewa wadda kake so ba ta fita daban a cikin su ba. Duk abin da sauran ƙawayenta suka ce a kanka da shi za ta yi amfani.

6. BARKWANCI: Idan ka kasance mai raha ga masoyiyarka to nan da nan za ka sace zuciyarta. Misali ka riƙa ce mata a duk lokacin da ka zo hira da ita, amincin so gareki ya tauraruwan zuciyata, ɗaya tamkar da goma cikin sahun mataye, a do da kyau siffarki ce, murmushinki ke sanya zukata fara’a. gimbiya adon ‘yan mata. Da sauran su. Kana mai ambaton haka cikin murmushi da shauƙi irin na soyaya kuma dole ne hirarku ta kasance mai amfani ba ka yi ta zuba ba, har sai ka gundure ta. Yawan magana ba shi da tasiri a soyayya muddin ba magana ne masu ɗauke hankali da san ji ko rashin gundura ba.

7. KUƊI DA KULAWA: Mata suna son samun saurayi mai tashen kudi da kulawa cikin bukatunsu a koyaushe. Idan ta samu wanda ya haɗa waɗannan abubuwa kuma ya tafiyar da su yadda ya kamata, to abu ne mai sauƙi ya sace zuciyar budurwa. Akwai mazan da suke roƙon ‘yan matansu kuɗi; wannan ba soyayya ba ce, sai a kira shi a kwaɗayi.

8. KYAUTATAWA: Sai dai kuma duk da na yi bayani kan cewa kwaɗayi bashi da kyau a soyayya, hakan ba shi yake nuna ba za ka kyautatawa masoyiyarka ba. Hasali ma idan kai haka, to za ka ƙara ƙarfin shaƙuwa ne tsakanin ku da juna. Sai dai idan za a yi kyautaa duba me masoyiya take da buƙata a daidai wannan lokaci. Misali, kar ka kawo mata hoda a lokacin da take buƙatar turare, atamfa, yayin da ita kuma leshi take so.

Sanin haƙiƙanin abin da budurwa ke so, ko da ku fara soyayya da ita, ko ba ku fara ba, yana taimakawa ƙwarai wajen sace zuciyarta.

Samfurin Kalaman Soyayya

Masoyiyata, ina son ki fiye da yadda kike so na. Ina son kasancewa tare da ke domin kina farantawa zuciyata.

Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Ke ce farin cikina. Ina nan riƙe da amanar soyayyarki har ƙarshen rayuwata. Na saka a raina ba zan taɓa mantawa da ke ba.

Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke ƙawatu wa da kallonsa, hanci ya ji daddaɗan ƙamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba.

Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata.

Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke lambun zuciyata
Kasan cuwar mu na ‘yan adam a doran ƙasa, Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu. Saboda haka samarin da suke ƙoƙarin ganin mallakan zuciyar ‘ya mace ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyin guda takwas da ake bi don sace zuciyar budurwa.

soyayya Ce zallah

 

Sarauniyata taho gare ni ki kama hannuna ki furtamin kalmar kauna a cikin kunnuwana…na rayu saboda ke ki zo ki mutu a kai na…ki sani ni fa ko a lahira idan an tashe mu to ke nake so a matsayin matata….na samu biyayyarki me kuma ya rage zan roka a wajen ubangiji?

kawai numfashi nake so ga ubangiji don mu yi soyayya mai dorewa ni da ke….fatana Allah.ya tsawaita mana rayuwa ya ke abar kaunata…wacce nake ganin sunan ‘ya’yan da zan haifa a cikin idanuwanki….fakina da idanuwana ba za su iya fada miki ko kwatanta miki adadin son da nake miki ba don tuni na shide a cikin sonki, na zama ke….




Ke dai taho gare ni dauke da kauna za ki gane ni ne na ki..ba ni da ta cewa sai godia ga Allah da ya ba ni yar fara mai fararen idanuwan da suka dace da kyakkyawan hancinta wanda ya yi daidai da kyakkywan kumatunki…wanda ya sa kika zarce sauran mata a kyau.

Ya ke mai kyakkyawar kirar jikin da babu irinki..mai iya kwalliya tamkar dawisu..mai zakin murya kamar kanari..takawarki lafiya mai tafiyar aasaita tamkar jimina kin isa ne dole ki yi domin duniya ban ga kamar ki ba ko kusa babu ba aiba kuma ba za ai ba

Ya ke rayuwata na dauki amanarki daga nan har izuwa ranar tashin alkiyama, ya ke wadda saboda tsananin kyauta idan tana tafiya ba takalmi samaniya ke ji kamar ta sakko kasa ki takata don ta ji me doran kasa ke ji.

Ke dai bari kawai ki sha kuriminki ni na ki ne ke tawa c,e kuma mun riga mun yi alkawari…ni da ke ke da ni jiki biyu ne muka zama rai daya zuciya daya…ba rabuwa har abada wannan shi ne alkawarina fatana ga mahalichchinmu ya cika mana burinmu. Sarauniya rife bakinki ba sai kin ce komai ba zuciyarki da gangar jikinki da kyawawan fararen idanuwanki su riga sun sanar da ni irin tsananin son da kike min don haka kwantar da hankalinki ba sai kin fada ba na san ba zai kwatantu ba ke dai samu guri mai kyau a cikin zuciyarki ki kara boye ni kawai domin ni na ki ne ke kadai

Hanya daya da zan bi na kwantar miki da hankali ita ce abin da kin riga kin sani kuma zan kara jaddada miki shi ne…..idan ba ke ba ni idan ba soyayyarki ba nimfashina duk wata ya budurwa a idanuwana fanko ne domin ke kadai nake gani na san na ga ‘ya mace kin ga idan ba ke a tare da ni ba zan iya gane ni da namiji ba ne don haka ni na ki ne mai sonki har abada soyayyarki ce jagorar rayuwata matukar ba soyayyarki to ba zan amfana ba kidai rike ni amana, ni ne dai na ki wanda ya zama ke, kika zama shi.
M asoyiyata abar kaunata ki sani ina sonki ina kaunarki son da nake miki har ya kai ga…..ko da idanuwana a rife suke ke nake gani idan na bude su ke nake son gani. Ko da ba na tare da ke ina jin motsinki a cikin jikina Lokachin da nake tinaninki, kadaici shi ya fiye min komai dadi. Me ya sa kina rayuwa a cikin jikina ni ma ina rayuwa a cikin jikinki amma duk da haka nake jin tsakaninmu da nisa?

soyayya ce

  Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda uku 1,2 da 3.



Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan kaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika boye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya kin ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena. Duk wani taku da na yi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min suka.

Ganinki burina, idanuwana ko bacci na farka ki amshi soyayyata abadan kada na koka ba ni barinki cikin kunci yaki zo na yi miki tarba. Daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa a duk zantukana sai na ambace ki. Damuwarki kullum tana cikin tinanina ke ce jin dadina kuma ke ce bacin raina ke kadai ce a zuciyata kalamaina, zabina jin dadina, bacin raina, saboda da ke kawai nake rayuwata, kaunarki ce ke kula da ni take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni ka san tuwata zan zamana a tare da ke har abada. Kamar yanda baki bai isa ya furta ba haka jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciya ta yi kadan ta kwatanta ruhinki ne kadai ya san yadda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowane dare ina sonki ba zan daina ba har abada saboda ban isa na daina ba.

Soyayyata da ke ba ta mutuwa kuma ba ta tsoran mutuwa koda za a yi mana kwace, ko da za mu mutu ko za mu lalace to soyayyar mu za ta kasance a raye na bayar da zuciyata na karbi ta ki na kamu da sonki. Ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da ta shagala a kan tsananin soyayyarki ka da rintsi ko zugar mahassada ya sa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke dankare a kan dan’adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake miki. 



Labarin Zainab Da Mubarak (7)

Har zuciyarsa ta burge ta sosai don ya iya tsari sai dai kuma ta san ba zai yiyu ta aure shi ba, cikin sauri ta kawar da wannan tunani ta ce “ai na za ta ba zuwa za kai ba, sai dai shi har yanzu ya kasa daina kallonta, shi ma kwalliyar da ta yi ta dauke hankalinsa gaba daya. Wani Material ta saka (Purple) wanda aka ratsa masa (pink colour) a jiki, dinkin riga da siket sai kuma ta dauko (pink) din mayafi ta dora a kai shi ma takalmin ya dace da mayafin jikinta, a hankali ya saki ajjiyar zuciya tare da murmushi ya ce “ Ni na Isa?, kin san ganinki ya fiye min komai” Sai fa ya zuba wa Zeey ido da colour da ke gefen precious wani irin wanda ya sa duk ta bi ta tsargu don kunya, ta sunkuyar da kanta ya ce “’yan mata adon gari, kin yi shiru, ko rowar muryar ake mana?” Ita dai Zeey colour ji take tamkar mafarki take yi, don ta tabbata duk wanda ya ga Seif dole ne ya yaba tsarinsa, precious ta yi gaskiya Saif yana da kyau sosai kuma gashi ya iya kwalliya don duk ya hada komai na kyau wanda ake bukatar a ga da namiji da shi, fari ne kyakkyawa na kin karawa, gashi dogo, hancinsa dogo, bakinsa dai-dai misali, idanuwansa gwanin ban sha’awa, gashin kansa akwance yake irin na Fulani.



Hasali ma ga iya furta zance sai dai kuma abin da ta lura da shi akwai jiji da kai hakan kuwa ba ya daga cikin tsarinta. Ta kale shi ta yi shiru na dan wasu dakiku kanar ba za ta yi magana ba, daga bisani kuma ta ce “Uhm..! Ya kake?, ya kuma hanya?”, Saif ya ce “ Lafiya lau, ina fatan dai kina kula min da baby na ko?” Ita dai Zeey colour har ta kagu tabar wajen ta koma ciki, a ganinta ya fiya kallo, a hankali ta danyi murmushi ta ce “Kamar ka sani, kullum ni nake kula da ita”, Precious kuwa har zuciyarta ji take kamar tafi kowa farin ciki don ganin gata ga Saif , cikin fara’a precious ta ce “ Wannan ita ce kawata Zainab ana kiranta da Zeey colour wadda nake ba ka labari ba ni da Aminiya kamar ta” Saif ya tsura mata idanu yanayin yanda take magana yana burge shi hakan ya sa ya ci gaba da saurarenta tare da bin kallon bakinta da yake motsi…

samfurin kalaman soyayya

 

Idan har na ce zan iya na yi karya domin ni kadai na san irin halin da nake ciki na rashin jin dadin tafiyarka.   Zuciyata na tafasa har nakan ji tamkar na fashe da kuka ka sani cewa, wannan sakon duciyata na sanar da kai, hannu aikinsa rubutawa ba wai ina fada ne don tsari ko don ka ji dadi ba.

Daga lokacin da ka hada yanaka-yanaka ka yi gaba ni ma daga wannan lokacin na tattara duk wani walwala na da farin ciki na na ajjiye su a can gefe barin da ba za su taba kusanto ni ba. Don haka ina sanar da kai ban yi fushi da abin da ka aikata ba kuma ban kiraka don ka bar abin da kake ba, illah na kira ka na ji laifin ba daga gare ni yake ba. Ka kasance cikin farin ciki ka huta lafiya. Na gode da kulawa, amma  ina ga ba ki kai ni shiga kewa da zullumi ba, dama an ce ba a sanin muhimmancin mutum sosai sai a lokacin da ya yi nisa da kai.Hakika jiya na kara gasgata wannan maganar.

Domin nisanta da na yi da ke na yini daya sai na ji kamar shekaru dubu ne, Kin riga kin zama fatar jikina duk wanda ya raba ni da ke kamar ya raba ni da kyauna kwarjini na hade da suturata. Ke garkuwa ce a gare ni mai kare ni daga abubuwa da dama, Hasken zuciyata farin cikin raina, annashuwa da jin dadi na. Ina sonki ina kaunar ki, ba zan iya nisa da ke ba. Ba zan bar ki ba duk rintsi duk wuya, Sai dai in ke kika bar ni  zuciya kuwa ba ta fatan ko mafarkin hakan balle a gaske. Ina so ki sani cewa soyayyarki ta yi nisa cikin zuciyata.

A hankali – a hankali ina ta ba ki filayen zuciyata ina so in rasa kaina a garin yin hakan ta yadda ba zan taba samuwa ba da sannu sannu dai ina ta mika rayuwata izuwa gareki ya masoyiyata kinzama abar kaunata wannan duk saboda karamcin kine a gare ni a yayin da nake kara kusantuwa dake duk tunane-tunane na suka fara bayyana ya masoyiyata kin zama abar kaunata kamar giza-gizai haka kika zamo inuwa a gare ni kamar ruwan sama haka kika jike ni da farin ciki kamar iska haka kika tafi da tunani na kin sabunta kaddarata ta hanyar samar da sabuwar safiya a rayuwata.

Dake kawai nake son kare rayuwata ya masoyiyata kin zama abar kaunata Kada ki taba mantawa da cewar wani na rayuwa ne kawai saboda ke ko ina zaki je ki tuna da hakan wani na rayuwa ne kawai saboda ke a duk inda kike ina miki fatan aminci addu’ar da zuciyata keyi kenan tamkar kyakkyawar abokiyar alaka haka rayuwa take idan kina tare dani a duk lokacin da kika yi nesa dani rayuwar sai ta zame mun ba dadi irin son da nake miki ta yaya zan iya bayyana shi wadannan idanuwan nawa tsahon dare suna tsayawa cur! kuma sunayin kuka duk da kasancewar ina tare dake me yasa nake jin kewarki? na kasa fahimtar miye hakan ki fada mun har na same ki duk da haka ina nesa da ke.


Yayin da kika iso bakin kofar zuciyata na sadaukar da rayuwata ga sunanki na koyi yadda zan rayu masoyiyata ada ban taba koyon yaya zan rayu ba ban taba koyon yadda zan rayu ba tare dake ba, masoyiyata wadannan yabo ne na gaskiya nake miki da zuciyata yayin da na same ki sai duniyata ta kawatu matuka duniyata ta cika burinta duk kanmu ba a ciki muke ba yanzu ne da muka hadu muka zama daya.
Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske. Haske a idanuwa na, Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba. Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki y ziyarci zuciya ta wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala.

yadda zaka ci rivar zama da mace

   Imamu Ahmad (RA) ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za su taimaka wajen zama da mace lafiya.
Yace ya kai da Na, hakika ba zaka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da zaka mu'amalanci matarka dasu don haka ka kiyaye su
NA DAYA DA NA BIYU:
Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da kauna
NA UKU: Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakaninku
NA HUDU: Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayinka
NA BIYAR: Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkinsa
NA SHIDA: Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bats zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su
NA BAKWAI: Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankali

Tuesday, January 29, 2019

A BIYO MU A LITTAFI NA GABA.


Wani mai share cikin jirgin sama ne mai karambani bayan ya shiga jirgi don yin goge-goge kamar yadda ya saba, sai ya tarar da wani littafi mai taken: “YADDA AKE KOYON TUkIN JIRGIN SAMA A SAUkAkE.”
Yana bude shafin farko sai ya ga an rubutu “Idan aka danna, kaza da kaza, za a tayar da injin jirgi. Sai ya danna, injin jirgi ya fara aiki. Sai ya bude shafi na gaba, nan kuma aka rubuta “Idan aka danna kaza da kaza, jirgi zai fara tafiya, nan ma ya danna, jirgi ya fara tafiya.
Can da ya bude shafi na gaba, sai ya ga an rubutu “Idan aka danna kaza da kaza jirgi zai yi sama, nan ma ya danna jirgi ya tashi sama da shi. Da ya bude shafi na gaba, sai idonsa ya raina fata don ya ga an rubuta “Don jin yadda jirgi ke sauka sai a biyo mu a littafi na gaba!”

SAURAYI DA BUDURWA 1.
Wani saurayi ne da budurwarsa suka yi hira kamar haka:
Saurayi: Ladidi an tashi lafiya?
Budurwa: Ta yi biris kamar ba ta ji shi ba.
Saurayi: Ladidi an kusa daura mana aure amma har yanzu ba ki daina yi min wulakanci ba.
Budurwa: Ta sake biris.
Saurayi: Dama ba wani abu ne ya kawo ni ba illa in tambaye ki ko kin iya tuki. Domin ina son matata ta kware a tuki
Budurwa: Nan da nan ta amsa cewa Tanimu ke nan shi ya sa nake matukar sonka.
Saurayi: Uhmm…
Budurwa: To wace irin mota za ka saya min?
Saurayi: Mota kuma?
Budurwa: Eh mana, ba yanzu ka tambaye ni ko na iya tuki ba?
Saurayi: Ni fa tukin tuwo nake nufi don wani masoyina ne ya ba ni kyautar buhun masara.

SAI IN ZAMA 'DAN TASI KAMAR KA!

Wani dan tasi ne ya dauko yara daga makaranta, sai wani daga cikinsu ya yi ta surutu, yana karatun da aka koya masu a ranar, yana cewa: “Idan babana sarki ne, mamata sarauniya, zan zama yarima.” dan tasi ya damu kwarai,
sai ya ce wa yaron: “Idan babanka dan fashi ne fa, kuma innarka karuwa, kai kuma me za ka zama?” Sai (yaro) ya ce: “Sai in zama dan tasi kamarka!”

wani saurayi ne yana zaune a gaban gidan su sai yaga wata yarinya taxo xata wuce yana ganin ta sai yaji ta kwanta mishi aransa ae kuwa baiyi kasa a gwiwa ba yaje yayi mata sallama ta amsa mishi sai yace baiwar Allah idan baxa ki damu ba ina dan so ki bani 1minute xan danyi magana dake ne sai tace ba damuwa.... Malama agaskia baxan 6oye miki ba tunda na ganki sai naji kinyi min ma'ana naji ina matukar son ki a raina.... Idan baxa ki damu ba xanso naji sunan malaman... Kuma xanso da ki bani full Address naki... Tayi shiru na dan wasu seconds ba tare da tace komai ba... Tana juyo wa sai ta daga hannu ta shimfida masa mari tace haba malam ka kalle ni ka kalle ka kace wai ni kake so plz na wuce da sanin ka kaje ka nemi dai-dai dakai.... Ba tare da yace mata komai ba sai ya juya ya tafi abin yayi masa matukar ciwo a xuciyar sa amman haka ya danne xuciyarsa.... bayan kamar 2weeks haka yana xaune a gaban gida inda ya saba xama sai yaji anyi masa sallama cikin wata sassanyar murya sai ya amsa sallaman sannan kuma ya daga kansa domin ganin wanda yayi masa sallaman yana daga kansa sai yaga Ashe wannan yarinya ce wanda ya ta6a tare wa 2weeks da suka wuce... Sai tace bawan Allah nasan xa kayi mamakin gani na amman kuma ba abin mamaki bane... Tun randa wannan abu ya faru na kasa samun sukuni a cikin xuciyata... Na kuma kasa samun nutsuwa araina... Sai naji cikin ikon Allah bayan faruwar wannan Abu sainaji na kamu da son ka araina... kuma ni yanxu nayi nadama abin da nayi maka plz ina so ka yafe min kuma ina so ka amsa soyayyah ta.... Wai yanxu idan kaine hakan ta faru da kai wani irin Answer za ka bawa wannan yarinyar...???



An FASA kwai

*

**AN FASA KWAI***
Wani mutum ne yayi sabuwar amarya sai ya dauketa ya kaita wani hotel don suyi honey moon dinsu a chan, watau suci amarcinsu a tsanake inji sa'ad khalifa yakubu (sky) .
suna shiga hotel din sai mutumin ya ajiye amaryar tasa a falo don yaje reception ya biya kudin daki ya kar6o makulli. Zaman amaryar keda wuya sai wata karuwa tazo wurinta ta sameta tace "sannu 'yar-uwa naga waccan macucin mutumin kema ya kawoki nan ne ku kwana (ta nuna mijin) toh kar ki sake ya kwana dake bai biyaki ba (ta dauka itama karuwa ce) kiyi maza ki amshi kudinki tun da farko don guduwa yakeyi baya biya don ni shaida ce saboda munsha kwana dashi baya biyana. kuma ki tambayi kowace karuwa a hotel dinnan kiji don kusan duk ya nemesu suna kwana dashi yana guduwa baya biya. kema don naga baquwa ce baki san halinshi bane har kika biyoshi zaku kwana ya cuceki. gashi da shegen neman karuwan tsiya kamar bunsuru don ni tuni ai na gujeshi kar yasa mun qanjamau don naji ana rade-radin wai yanzu ya kamu da qanjaman don cikakken 'Dan-duniya ne"
*Wai in kece amaryar ya za kiyi tun baku tare ba? za kiyi kasada ne ku kwana sannan ki tabbatar ko kuwa ya ya???
*KIWON LAFIYA
(yadda zaka cire targade da kanka)
Ka sami igiyar kyalle mai karfi sai ka daure yatsar mai targade a wani turke kamar na rumfa, sai ka fizgi yatsan da karfi fizga daya idan kayi da kyau targaden zai fita. Yadda zaka gane fitarsa shine za kaji yayi qara 'qas' alamar ya fita ya gyaru kenan, sai ka sami mantaleta ka dirza a wurin targaden. Da safe ka gasa da ruwan zafi da tawul kasa mantaleta shikenan. Idan bai fita ba yayi qara ba sai ka sake kwatantawa har a dace shikenan.




BAZAZZAGI DA LARABCI.
Wani Bazazzagi ne suka hada kudi da Balarabe suka sayi jakai guda
biyu suna kiwo. Kuma ya kasance Bazazzagi ke yin kiwon wadannan
jakuna guda 2. Kwatsam wata rana sai aka yi ruwa ya cika gidan Bazazzagin nan, har jakunan suka mutu. Ya je ya samu Balarabe, yana so ya yi masa Bayanin cewa ruwa ya cika masa gida har jakunan sun mutu. Suna haduwa sai ya ce masa: “Wa himaruka wa himariy, al ma’u bulbula fiy baitiy, mautu jami’an.”

Wani bawan Allah me mai tsananin kamun kai


Wani bawan Allah ne mai tsananin kamun kai, wanda yake zaune a wani gidan haya da matarsa, sai watarana matarsa ta tafi unguwa shi kuma sai ya shiga bayi yayi wanka sai ya rataye tufafinsa akan katangar bayin don bayin budadde ne babu rufi. Sai wani 6arawo yaga tufafin sun leqo waje sai ya janyesu ya tsere ta lungu.
Mutumin bai tashi sanin an sace tufafinsa ba har sai da ya gama wankansa zai fito sannan ya ankara don haka sai ya tsaya shiru ya rasa abin yi don yaji motsin matar abokin zamansa tana kwashe shanyar tufafinta dafa shanya a igiyar shanyar dake tsakar gida kusa da bayin saboda tasowar iska kar ya zubar mata da tufafin. Ana cikin haka sai kuwa iskar ta dauki wani fallen zaninta ta jefa matashi bayi inda mutumin nan yake ciki.
Ai sai mutumin yayi murna ya dauki zanin matar wani ya daura don ya rufe tsiraicinsa dashi sai ya fito da sauri daure da zanin matar wani a qugunsa kuma gashi baya yin magana da matar auren gidan, sai ya nufi dakinsa da sauri ita kuwa mai zanin sai abun ya daure mata kai tana ta kallon zanin sallan da mijinta ya dinka mata a qugun wani mutum wanda ba mijinta ba.
Mutumin na isa dakinsa sai ya tuna ya ashe ya rufe dakin da makulli kuma makullin na cikin aljihun wandonsa da aka sace sai ya tsaya a jikin qofar yana salati don duk kayansa suna cikin dakin. Chan sai matarsa ta dawo unguwa taga mijinta da zanin matar hayar gidan sai ta tayar da rigima akan alanbalan yana neman matan gidan don su biyu aka bari a gidan kuma ga zani shaida a qugunsa don haka tabbas kwartanci yaje sukayi a dakinta har ya daura zaninta.
Ana cikin hayaniya sai mijin waccan matar da aka daura zaninta ya shigo yaga abin dake faruwa shima sai ya tayar da rigima har kotu da qyar Allah Ya fid da mutumin nan bisa shaidar tufafinsa da aka kaiwa wani dillali sayarwa shi kuma ya gane mai su don yasan ana rigimar shine ya kawosu kotu tare da yin cikakken bayanin da tasa aka kama 6arawon sannan aka wanke mutumin daga zargi.
*Ya Allah Ka qara tsaremu daga afkawa cikin kowane irin musibah, ameen.

Wata amarya CE



Wata amarya da mijinta sukaje bankin zenith domin su cire wani kudi. Ko da amarya tazo shiga se kawai muka ji wani alam me karfin gaske, jin haka se ga ‘yan sandan bankin su fito da gudu da bindigun su! Ai ina ganin haka se na tsure! Sun kamani ni da matata wai basu yarda damu ba shisa zasu kai ofishin ‘yan sanda sun bincike mu! Munje har anyi sacin dina amma basu ga komai ba! An zo kan matan ana sacin dinta kawai se ga gwangwanin milo babban ya fado daga kanta! Dani da ‘yan sandan ba wanda ze kama wani gurin gudu, domin kuwa mun dauka bom ne ya fado ashe wai acuci mazanta ne ya fado! Wannan jaraba dame yayi kama??? Shiko D.P.O be ma dawo cikin hayacin sa ba tsabar tsorata da yayi.

Jiya ina kwance da misalin karfe 2:30/am   na dare ina bacci sai na farka. Ina farkawa sai naji hayaniyar mutane a waje sai na fito amma banga kowa bahSai na koma daki na kwanta amma ban daina jin hayaniyar ba sai mah karuwa takeyi Na sake fitowa a karo na biyu but banga kowa bah.....Kamar ance in kalli sama,ina duba sama kuwa sai naga mutane Wai ashe jirgin sama ne ya lalace shine suke turawa Saura kuma kuce karya Nake.

Wata tsohuwa ce suka je kasuwa da karamin jikanta, sai jikan ya dauki motar wasa sai tsohuwa tace digiri ajiye motar nan, sai mai kaya ya tambayi tsohuwa: sunanshi digiri? Tsohuwa tace: mamanshi na tura   jami'a ta dawo min dashi

Wani saurayi yaje wajen buduewarsa




Wani saurayine yaje zance wajen budurwarsa , suna tsakiyar hira sai aka fara ruwa kamar da bakin kwarya har zuwa dare ruwa bai daukeba. sai baban yarinyar nan yace da ita "naga alama ruwannan ba mai daukewa bane yanzu,don haka ki gara masa dakin bakin nan sai ya kwana anan idan  Allah ya kaimu gobe sai ya koma. budurwar ta mike ta shiga gida don cika umarnin mahaifinta. bayan ta gama gyara dakin sai ta dawo don yiwa saurayin nata iso  amma abin mamaki sai ta tarar bayanan don haka ta koma ta sanar da babanta halin da ake ciki. uban ya rinka mamakin inda ya shiga ana cikin haka sai gashi ya shigo da gudu jikinsa ya jike jagab, da ganinshi sai uban ya tmbaye shi ina yaje haka cikin ruwannan? sai saurayin nan ya amsa da cewa"ai gida na koma na dwakko bargo saboda ko za'ayi sanyi cikin dare wai idan kaine uban yarinyar ya zakayi?

Wani yaro ne Budurwarsa ta gaiya ce shi Birth da y din ta sai yake tambayar Baban sa "me yakamata ya bata ?  Sai Baban yace "yaya Budurwar ta ke ? sai yaron ya fara fada masa  kamar haka :-

(1) Tana da kyau

(2) Tana da gashi

(3) Tana da Ido

(4) Ga ta siririya

(5) Ga jiki mai kyau

(6) Ga ta da Hips,

Kai Dad baka gan ta ba son kowa kin wanda ya rasa. Daga nan Baban yace kasan abin da za ka bata sai yaron yace a a. Sai Baban yace ka bata number ta .

Wani ustazu ne kullum yaje gurin budurwansa baida wani magana sai wa'azi ma'ana taji tsoron

allah ta bi duniya a hankali sai wannan budurwan tace ita ko sai ta gwada shi ta gani in mai tsoron

allah ne... dare nayi yazo gurin ta... suna cikin magana sai ta kama mai hannu..... ustazu yace "subhanallahi" ta rungume shi yace "alhamdulillahi" tai mai kiss yace masha'allah data sake shi yace astagfirullah.

Hahahhaha......!!!

Ustaz da mai tuwo



Akwai wata mata mai siyar da tuwo wadda ta kware wajen iya girki, matsalarta kawai masifa da ruwan bala’i.

Rannan sai wani Ustaz yazo cin abinci, da ya kammala cin abinci sai mai karbar kudi tace malam kudin ka dubu daya da dari daya.

A nan fa Ustaz ya kafe ya ce bazai biya ba domin kudin yayi yawa.

Yarinya da taga abu yafi karfinta saitaje gayawa Hajiya.

Tun daga wajen shago Hajiya ke danna zagi da masifa tace bari inga wane shege ne zai kawomin iskanci da raini.

Tana shiga shagon sai ta hada ido da Ustaz sai kawai tayi shuru ai sai takoma kan mai karbar kudi da masifa kefa baki da lissafi ai sai kiyi min bayani kice Mallam ne ai.

Sai tace kara mar Special Pack biyu ki hada masa da ruwan Swan guda biyu.

Mai aiki tayi shiru tana mamakin Hajiya.

Sai da Hajiya ta daka mata tsawa sannan ta dawo hankalinta… ta hada abinci tabawa Ustaz….

Hajiya sai ta fara cewa an gode Mallam Allah yasaka da alheri……

Ustaz na fita Hajiya ta fadi kasa tana hada uban gumi tana wani irin nishi…..

Sai mai aiki tace Hajiya lafiya kuwa…..

Hajiya tace baki gane shi ba? SHEKAU ne ai DAN Ubanki…

Buzu ya gamu da gagarumin barawo



Wani Buzu ne falke, ya rika bugun gaba yana cewa shi babu wanda ya isa ya yi masa sata.



Ashe wani babban barawo ya ji haka, don haka sai ya sha alwashin sai ya yi masa sata.



Wata rana an ci kasuwa, Buzu ya sayar da kayansa duka, sai barawon nan ya sace masa kudi, ya bar shi da rakumi kadai, sannan kuma ya yi masa aski kwal-kwabo, a lokacin da yake barci.



Da safe, Buzu ya tashi ya ga cewa an yi masa sata sai ya yi ta mamaki, yana cewa: “Ni din ne za a yi wa sata? Can sai ya shafa kansa ya ji ba gashi, sai ya ce: “Haba, ashe ma ba ni ba ne!”


Sansanin Dan kano a kaduna



Wani Bakane ne daga Kano ya zo Kaduna bakunta, sunansa Sabo.
Da ya fita wajen kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi,

Sai ya ji masu bas- bas suna cewa: “Sabo, Sabo, Sabo” (Suna nufin Unguwar Sabon Tasha).

Shi kuma sai ya dauka shi ake kira.

Da an ce “Sabo,” sai ya waiwaya yana daga hannu.



Da ya koma gida sai ya rika cewa: “Ashe ni sananne ne a garin Kaduna, Domin da na je kasuwa, duk inda na waiga sai na ji ana cewa, Sabo, Sabo, Sabo!”






Wani Abu sai bazazzazagen tela



Wani Bazazzagen tela ne surikinsa ya ba
shi dinki, sai ya sanya masa ranar da zai zo ya karba.


Da ranar ta zagayo, Sirikin ya zo karbar dinki, sai ya kasance tela bai gama dinki ba. Sai telanka ya ce da surukin nasa: “Baba ka yi hakuri, ban dinka ba amma ka dawo gobe ka karba.


Ashe wajen rufe shi sun mance ba su rufe kafafunsa ba.


Da surikin ya karaso shagon, sai telolin suka isar da sako kamar yadda tela ya bari.


Surikin ya yi kamar ya yarda, ashe ya ga kafafun telan a waje, sai ya ce wa telolin: “Ku shaida masa cewa nan gaba idan zai yi tafiya, ya daina tafiya yana barin kafafuwansa.”

Inyamuri a zaman kotun hausawa


Wani Inyamuri ne ya halarci zaman kotu sai kuwa ya yi sa’a a ranar ana zaman sauraron karar wata mace da aikata zamba.

Da aka kammala sauraron karar sai Alkali ya yanke wa matar hukunci daurin shekaru biyar ko kuma tarar Naira dubu dari biyu da hamsin.

Sai Alkali ya yi tambaya da cewa za a tafi da matar gidan kaso amma idan har da akwai wanda zai tsaya mata, to fa za ta iya samun ‘yancinta.

Inyamiri ya dubu ya ga babu wanda ya mike ya ce zai tsaya wa matar nan,

Sai ya ce a ransa “Hausa mugu ne walayi, zai bari wannan mutum ya yi cekala biyaru a prison saboda tsayawa”

Sai ya mike tsaye ya ce “Alkali, Mun saya mishi”

Sai Alkali ya ce to tunda an samu wanda zai tsaya mata ba za a kaita gidan kaso ba. Kai kuma ya ya sunanka? Alkali ya tambayi Inyamiri.

Inyamiri ya masa da sunanmu ne Chinedu.

Sai Alkali ya ce to, za ka biya tarar Naira dubu dari biyu da hamsin don wannan baiwar Allah ta samu ‘yancinta kamar yadda ka fada cewa ka tsaya mata.

Chinedu ya ce “Mene ne?”

Alkali ya ce Naira dubu dari biyu da hamsin

Chinedu ya ce ” Na two hundred and fifty thousand naira be that oo”

Alkali ya kwarai

Sai Chinedu ya ce “Oga Alkali, mun zauna mishi…kai munkwanta mishi”

Idan INA yi INA so naga kowa manayi


Wani shakiyin Bazazzagi ne ya yi dinkinsa babbar riga mai asake akan wata dalleliyar shadda ruwan kwai. Da ka ganshi ka ga mai hannu da shuni. Ai kuwa sai ya nufi gidan abinci (Restaurant), ya samu waje ya zauna ya kwalawa mai restaurant kira da karfi ya ce “Hado min plate na Naira 2,000 kuma ki hadawa kowa da ke wajen nan plate na Naira 3, 000 saboda idan ina cin abinci, ina so naga kowa yana ci”.

Duk mutanen da ke wajen suka fara godiya yayin da mai restaurant ta zubawa kowa nasa ta kawo masa hadin girma. Shinkafa da dankalin turawa da farfesun kayan ciki ko kifi ko naman kai, ya dai danganta da abinda mutum ke so. Kana ga hadin kwadon kayan lambu da a turance a ke kira da salad

Bayan mutumin ya gama cin abinci sai ya kuma cewa mai abincin “kawo min abin sha na Naira 500 kuma ki baiwa kowa na Naira 1, 000 saboda idan ina shan abu, ina so naga kowa yana sha”.

Mai Restaurant ta kaiwa kowa kayan shaye-shaye kala-kala. Nan fa mutanen wajen suka barke da shewar “Allah ya kiyaye ka!”

Bayan mutumin ya gama sai ya cewa mai Restaurant “kawo min resit na biya kudina kuma ki kaiwa kowa nasa resit ya biya kudinsa, saboda idan ina biyan kudina ina so naga kowa yana biyan nasa”.

Yanzu haka mutumin yana kwance a asibiti saboda dan karen dukan da masu gidan abinci da kuma mutanen da ya saka suka ci abincin da basu yi niyya ba suka yi masa

Yanzu haka ni kuma ina kwance ina dariya, saboda idan ina dariya ina so na ga kowa na dariya

Mai kalangu da mahaukaci

Wani mahaukaci ne yasa shadda mai kyau kamar me hankali yaje daurin aure sai yaga wani Mai kalangu yana yiwa mutane kirari ana bashi kudi.

Sai maukacin nan ya cewa mai kalangu “nima jinin sarautane, ya kamata a yi min kida”

Sai me kalangu da yaransa hankalinsu yakoma kan maukacinnan suka rude da kida suna cewa “dan sarki jikan sarki”

Sai mahaukaci yacewa mai kalangu anbaka mota yaranka suma anbasu mota

Mai kalangu ya ce “yaushe zamuje mu amso?”

Sai mahaukaci ya ce “sai randa kalangu yafashe”

Nan ta ke mai kalangu ya sa wuka duk ya fasa kalan gunansa

Sai mahaukaci ya ce “shima kalangu an bashi mota”

Mai kalangu ya ce “amma mallan bakada hakali ko?”

Sai mahaukaci ya ce “hankali shima anbashi mota”

Mai kalangu yace mal Allah baka lafiya

Sai mahaukaci ya ce “lafiya itama anbata mota” kai!

Hira tsakanin saurayi da budurwa

Wani saurayi ne yaje wajen budurwar sa hira suna cikin hirar sai NEPA suka kawo wuta sai ya tambaye ta yace yanaga ko, ina da wuta amma banda gidan ku?


Sai tace wlh lokacin ana ruwan sama shine iska ta tsinke WAYAR. Sai yace to meyasa baku kira YAN NEPA sun
gyara ba?

Sai tace, wallahi mun kira su sunce zasu zo gashi yau har kwana biyu shuru. Sai yace bakomai, abinda za,ayi shiga gida kisa YARA SU FITOMIN DA TSANI DA KUMA FILAYA.


Sai tace haba kawai ka barshi za,a gyara, SWEET HEART kaga ba aikin ka bane. sai yace haba MY LOVELY ai abun duk bigene.

Aka fitomai da TSANI DA SAURAN KAYAN AIKI ya hau FALWAYA ya fara aiki. Can zuwa wani dan lokaci sai budurwar sa taji yayi wani MUGUN IHU HADE DA KARA wuta ta jaho sa kasa ya fado cikin KWATA A SUME.


Bayan ya farfado daga suman da yayi, ya tashi zaune yana daga kansa sai yaga budurwar sa da baban ta da babarta da yaran gidan gaba daya da kuma sauran yaran unguwar suna mai sannu.



Can saiji yayi wata karamar yarinya kanwar budurwar sa tace, LA! AUNTY SAURAYIN KI YAYI KASHI A WANDO.
Hahahaha!