Tuesday, January 29, 2019

Mai kalangu da mahaukaci

Wani mahaukaci ne yasa shadda mai kyau kamar me hankali yaje daurin aure sai yaga wani Mai kalangu yana yiwa mutane kirari ana bashi kudi.

Sai maukacin nan ya cewa mai kalangu “nima jinin sarautane, ya kamata a yi min kida”

Sai me kalangu da yaransa hankalinsu yakoma kan maukacinnan suka rude da kida suna cewa “dan sarki jikan sarki”

Sai mahaukaci yacewa mai kalangu anbaka mota yaranka suma anbasu mota

Mai kalangu ya ce “yaushe zamuje mu amso?”

Sai mahaukaci ya ce “sai randa kalangu yafashe”

Nan ta ke mai kalangu ya sa wuka duk ya fasa kalan gunansa

Sai mahaukaci ya ce “shima kalangu an bashi mota”

Mai kalangu ya ce “amma mallan bakada hakali ko?”

Sai mahaukaci ya ce “hankali shima anbashi mota”

Mai kalangu yace mal Allah baka lafiya

Sai mahaukaci ya ce “lafiya itama anbata mota” kai!

No comments:

Post a Comment